Babban bankin Najeriya CBN ya bayar da umarnin dakatar da cirar haraji ga mutanen da su ke son ajiye kuɗi tsakanin naira dubu ɗari biyar zuwa sama.

Mai riƙon muƙamin daraktar sanya idanu Adetona Adedeji ce ta sanar daa haka a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunta da aka fitar ranar Litinin.

Bankin ya dakatar da cirar haraji a kan masu ajiye kuɗi da ya haura naira 500,000 har zuwa watan Afrilun shekara mai zuwa.

A baya bankin ya bayar da umarnin cirar haraji ga masu ajiye kuɗin ne da nudin rage yawan amfani da takardun kudi.

Sai dai ana zargin hakan ba ya rasa nasaba da ƙarancin takardun kuɗi da ake fama da su musamman a wasu jihohin ciki har da Abuja.

Bankuna sun takaita bayar da kuɗi ga abokar hulɗar su a ciki da wajen bankuna.

Yayin da wasu injinan cirar kuɗin ma ba a samu a wasu bankunan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: