Al’ummar karamar hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara sun nemi daukin ma hukunta, bisa yadda ‘yan bindiga ke addabar yankin da hare-hare tare da ci gaba da mamaye yankin.

Al’ummomin sun bayyana cewa koda a makon da ya gabata sai da ‘yan bindigar su ka kai wasu hare-hare garin har sau hudu, inda suka hallaka mutune uku da wasu 16, tare da kona ofishin ‘yan sanda da motocin soja guda biyu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a yayin harin wasu jagororin ‘yan bindigar guda biyu Sani Black da Sani Dan Karami ne suka jagoranci kai hare-haren yankin.

Wani mazaunin garin mai suna Auwalu Musa ya ce koda a jiya Lahadi sai da ‘yan bindigar suka sake komawa kauyen, inda suka yi garkuwa da wasu mata hudu.

Shi ma wani mazaunin garin ya bayyana cewa ‘yan bindigar na kai’wa garin harin ne sakamakon sojoji sun kwato musu dabbobinsu a wani hari da suka taba kai’wa kauyen.

Mazaunin garin ya kara da cewa sojojin sun kwato dabbobin ne daga hannun Sani Black.
Kazalika ya ce koda a ranakun Asabar da Litinin sai da sani Black ya kai hari garin domin daukar fansa.

Mazaunin garin sun bayyana cewa yawaitar hare-haren ‘yan ta’addan ya sanya wasu da dama dake cikin garin yin hijira zuwa wasu garuruwan domin kaucewa hare-haren ɓata-garin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: