Rundunar yan sandan Jihar Legas ta samu nasarar Kama wani magidanci da ya hallaka matarshi bisa kin girka masa abincin da ya fiso.

Lamarin ya faru ne tun a ranar Alhamis 14 Disamban da muke ciki, a yankin Olota da ke cikin karamar hukumar Alimosho ta Jihar.
Rundunar ta bayyana cewa bayan dawowar mijin matar daga aiki ne ya tarar da matar tashi ta dafa Taliya, hakan ne ya sanya ya dauki mummunan matakin akan ta.

Rundunar ta Kara da cewa kanin wadda aka kashe ne ya shigar da Kara gaban ofishin ‘yan sanda a yankin,bayan ta rasa ranta a hanyar zuwa Asibiti.

Rundunar ta ce ya zuwa yanzu an aike da wanda ake zargin zuwa,sashin binciken laifuka na Jihar,domin gudanar da bincike akansa.