Kotun daukaka kara da ke zaman ta a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da nasarar tsohon gwamnonin Jihar Sokoto Aliyu Wamako a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar Sokoto ta Arewa a jam’iyyar APC a zaben 2023.

Sannan kotun ta kuma tabbatar da nasarar Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben sanata mai wakiltar Sokoto ta kudu.
Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Talata, bayan da Ibrahim Danbaba ya shigar da kara gaban kotun yana mai kalubalantar nasarar Tambuwal, inda shi kuwa tsohon mataimakin gwamnan Jihar Manir Dan’iya ya kalubalanci nasarar Aliyu Wamako a gaban kotun.

Kotun ta yanke hukuncin ne karkashin alkalai uku bisa jagorancin mai shari’a Mustapha Muhammad.

Bayan yanke hukuncin farko mai shari’ar yayi watsi da karar da Danbaba ya shigar gaban ta,yana kalubalantar mai kalubalantar Tambuwal, inda kuma Kotun ta ci tararsa Naira dubu 500,000.
Sannan kotun ta sake yin watsi da karar da Dan Iya ya shigar gabanta, inda shima yake kalubalantar nasarar sanata Wamako.
Alkalin ya bayyana cewa mutanen ba su da wasu gamsassun hujjoji akan karar da suka shigar gaban nata.