Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta Kama wasu mutane biyar da ake zargin su da mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Abubakar Sadik Aliyu ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema Labarai.


Abubakar ya ce an Kama mutanen ne a kauyen Kurmi da ke karamar hukumar Bakori ta Jihar, dauke da bindiga kirar AK47.
Aliyu ya ce sun Kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri da suka yi akansu da taimakon jami’an Sa-kai.
Kakakin ya Kara da cewa dukkan wadanda ake zargin sun fito ne daga Kauyen Kakumi da ke karamar hukumar ta Bakori a Jihar.
Kazalika ya ce wadanda ake zargin sun hada da Kasamanu Abdullahi, Abdulrahman Shu’aibu, Abubakar Tukur, Sarhabilu Dahiru, da kuma Sulaiman Sunusi.
Ya ce a yayin bincikar su sun bayyana cewa sun sace bindigun ne daga gurin wani mai suna Jamilu Lawal, inda kuma rundunar ta gayyace shi domin amsa mata tambayoyi.