Wani bincike da wani kwamiti ya gudanar karkashin jagorancin Jim Obaze, akan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya gano cewa tsohon gwamnan bankin ya boye wasu kudade a asusun ajiya guda 593 a kasashen ketare.

Jagoran kwamitin Obaze ya ce ya gano kafatanin bankunan da Emefiele ya ke ajiyar kudaden a ketare.
Sannan ya ce bayan kammala binciken da kwamitin ya gudanar ya gabatar da rahoton binciken ga shugaban Kasa Bola Tinubu.

Obaze ya kara da cewa a yayin binciken an kuma gano hannun wasu daraktocin bankin su 12 a cikin lamarin.

Kwamitin ya kara da cewa koda a gurin buga sabbin kudi da aka yi a baya Emefiele ya Saba doka a wajen bugawa.
Ana zargin Emefiele ne da boye kudaden a Kasashen Birtaniya, Sin, Amurka, ba tare da amincewar shugabannin bankin na CBN ba.
Bayan mika rahoton binciken ga shugaban Kasar, ana sa ran gwamnatin tarayya za ta kara tuhumarsa da karin wasu laifukan a gaban kotu