Wasu yan bindiga sun hallaka mutane 145 a hare-hare da suka kai kan kauyuka 23 a jihar Filato.

An ruwaito cewa yan bindigar sun kashe mutum 113 a kauyuka 20 a karamar hukumar Bokkos da wasu 32 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Barikin Ladi.
An ruwaito cewa an farmaki kayukan ne daga daren ranar Asabar zuwa safiyar Litinin.

Har ila yau, an ruwaito cewa hare-haren ya kuma jikkata daruruwan mutane da lalata kayayyaki.

Lamarin ya shafi kauyukan Ruku, Hurum, Darwat, Mai Yanga Sabo da NYV a yankunan Gashish da Ropp.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Bokkos, Monday Kassah, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a jiya Litinin.
Da aka tuntube shi don jin ta bakin sa, kakakin yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai amsa sakon waya da aka tura masa ba.
Sai dai kuma, Kyaftin Oya James, kakakin Operation Safe Haven, da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar, ya tabbatarwa jaridar Daily Trust da faruwar lamarin.
Sai dai kuma, bai tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ba a yanzu, amma dai ya ce zuwa yanzu an daidaita lamarin.