Gwamnan jihar Kono, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya damƙa kananan yara bakwai a hannun iyayensu, waɗanda aka sato daga jihar Bauchi.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da kakakin gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Jumu’a, 29 ga watan Disamba, 2023 a Kano.

Gwamnan ya nuna matukar bacin ransa game da abinda ya faru har aka sace ƙananan yaran guda bakwai daga Bauchi sannan aka yi safararsu da sayar da su a jihohin Anambra da Legas.

Abba Gida-Gida ya yi mamakin yadda tawagar masu aikata laifin suka ƙware wajen sace ƙananan yara daga jihohin arewa tare da zuwa can wani wuri su sayar da su.

Sannan gwamnan ya yabawa namijin kokarin rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴan sanda, CP Muhammad Hussain Gumel.

A cewarsa, kokarin dakarun ƴan sanda ne ya yi sanadin kama masu safarar kananan yaran tare da ceto waɗannan guda takwas.

Ya kuma bukaci iyaye da su kasance masu taka-tsan-tsan da kula da lafiyar ‘ya’yansu a matsayin babban nauyin da Allah ya ɗora musu.

Gwamna Abba Kabir ya kuma yi kira ga takwaransa na jihar Bauchi, Bala Muhammed, da ya dauki kwararan matakai na shari’a a kan wadanda ake zargin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: