Gwamnatin Najeriya za ta Kara tsawaita dakatar da tantancewa da kuma karbar takardun shaidar kammala karatun digiri daga wasu jami’o’in kasashen ketare, bayan dakatar da jami’o’in Togo da Benin.

 

Ministan ilmi a Kasar Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a yayin wata fira da gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

 

Ministan ya ce bayan dakatar da jami’o’in Benin da Togo gwamnatin kasar ta sake dakatar da jami’o’in jamhuriyyar Nijar, Uganda, da kuma Kenya.

 

Mamman ya kara da cewa gwamnatin na ci gaba da gudanar da binciken irin wadanan jami’o’i da ke aiki a Kasar domin dakatar da su.

 

Dakatarwar da gwamnatin ta yiwa jami’o’in na zuwa ne bayan bayyanar wani rahotan samun takardun karatun digiri na bogi cikin Kasa da watanni biyu, ba tare da shiga aji ba akan kudi naira dubu 600 daga jamhuriyyar Benin.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: