Gwamnatin Najeriya ta amince da kamfanonin Air Peace, Max Air da kuma Flynas na kasar Saudiyya da su yi jigalar maniyyata aikin hajjin bana.

 

Gwamnatin ta kuma sake amincewa da kamfanonin Cargo Zeal Technologies Limited da Nahco Aviance, da kuma Qualla Investment Limited, da su yi jigilar dakon kayan maniyyatan daga Kasa mai tsarki.

 

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan yada labarai na hukumar jindadin Alhazai na Kasa NAHCON Fatima Sanda Usara.

 

Sanarwar ta bayyana cewa kamfanin Air Peace zai yi gilar maniyyatan Jihohin Akwa Ibom, Abia, Bayelsa, Anambra, Cross River, Ebonyi, Delta,Edo, Ekiti, Imo, Enugu, Kwarai, Ondo, Rivers da kuma birnin tarayya Abuja.

 

Sanarwar ta ce Kamfanin Flynas zai yi jigilar maniyyatan Jihohin Borno, Sokoto, Neja, Yobe, Zamfara, Legas, Osun kuma Ogun.

 

Sanarwar ta Kara da cewa kamfanin Max Air zai yi jigilar maniyyatan Jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Bauchi, Gombe, Nasarawa, Kogi, Kaduna, Taraba, Adamawa, Filato, Benue da kuma Oyo

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: