Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da Kama mutane 2,931da ake zarginsu da aikata laifuka daban-daban a Jihar a shekarar 2023 da ta gabata.

 

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Muhammad Husaini Gumel ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da ƴan jarida.

 

Gumel ya ce mutanen ana zarginsu ne da laifukan fashi da makami, garkuwa da mutane da hallaka su da kuma sauran wasu laifukan.

 

A cewar kwamishinan dukkan mutanen da aka kama an kamasu ne a kananan hukumomi 44 da ke fadin Jihar.

 

Gumel ya kara da cewa mutane 337 an kamasu ne da laifin aikata fashi da makami, yayin da 55 kuma da laifin yin garkuwa da mutane.

 

Kazalika ya ce an kuma Kama 65 da aikata dillancin miyagun kwayoyi, 68 da aikata satar ababan hawa, damfarar mutane da kuma aikata daba.

 

Sannan ya kara da cewa jami’an rundunar sun kuma kubatar da mutane 25 da aka yi garkuwa da su, yayin da 63 aka karbo su daga masu safarar mutane, sannan rundunar ta karbi tubabbun ‘yan daba 662.

 

Kwamishinan ya ce an kuma kwato makamai daban-daban ciki harda bindiga kirar AK47 guda hudu.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa dukkan mutanen da suka kama sun gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukunci.

 

Daga karshe yayi Kira ga Al’ummar Jihar da sh ci gaba da bai’wa rundunar hadin Kai domin kawo karshen batagari a Jihar

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: