Hukumar ya ki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon EFCC ta karbe fasfon Ministar jin kai da shugaban kasa ya dakatar watau Betta Edu.

Haka zalika an karbe takardun fasfon Hajiya Sadiya Umar-Farouq wanda ta rike wannan kujera tsakanin 2019 da 2023.

Dr. Betta Edu ta ziyarci hedikwatarta EFCC a Abuja ne da kimanin karfe 10:00 na safiyar Talata domin amsa tambayoyi daga jami’ai.

Har zuwa karfe 7:00 na yamma, an tabbatar da Betta Edu ta na hannun hukumar EFCC.

Dakataciyyar ministar ba ta bada wani uzuri kamar yadda Sadiyar Umar-Farouq ta yi a makon jiya ba, nan ta ke ta mika kan ta ga hukuma.

Rahoton ya ce an yi kusan awanni 12 ana yi wa Sadiyar Umar-Farouq a kan zargin wasu N37.1bn da aka karkatar a lokacin da ta ke ofis.

Kafin a bada belin tsohuwar ministar, sai da aka tabbatar an raba ta da takardunta.

Wata majiya ta ce haka aka yi da Betta Edu saboda EFCC ta tabbatar da cewa jami’ar gwamnatin ba za ta tsere yayin da ake bincikenta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: