Kungiyar Dattawan Arewa reshen jihar Kano ta fusata da samamen da EFCC ta kai ofishin kamfanin Dangote a Legas.

 

Kungiyar ta ce wannan samame zai kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya gaba daya.

 

Sakataren yada labaran kungiyar Bello Sani Galadanci shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a Kano a jiya Laraba 10 ga watan Janairu.

 

Sanarwa ta ce Kungiyar Dattawan Arewa da jama’ar jihar Kano sun kaɗu da samame da EFCC ta kai a ofishin kamfanin Dangote.

 

Wannan samame ya biyo bayan binciken da ake yi kan wasu kamfanoni 52 da sha’anin canjin kudade ya shafa cikin shekaru 10.

 

Kafin kai sumamen, Kamfanin Dangote ya nemi bahasin me yasa ake bukatar takardun amma sai da sukaje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: