Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ta kammala duk wasu shirye-shiryen gudanar da zaɓukan cike gurbi na ƴan majalisar dokokin jihar.

Zaben cike gurbin mambobin majalisar da INEC zata yi a Kano sun kunshi mazaɓun Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garin Malam da Rimin Gado/Tofa.


jaridar Punch ta ruwaito cewa, INEC ta tsara gudanar da zaɓukan cike gurbi ne ranar 3 ga watan Fabrairu, 2024.
Kwamishinan zaɓe na jihar Kano, Abdu Zango, ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a ofishin INEC na Kano ranar Talata.
Ya ce tuni hukumar INEC ta aike da kayan zabe masu muhimmanci da sauran su ga dukkanin kananan hukumomin da abin ya shafa.
Zango ya ƙara da bayanin cewa za a yi amfani da na’urar BIVAS a yayin zaben cike gurbin da nufin tabbatar da an yi sahihin zabe kuma ingantacce.
Kwamishinan zaben Kano ya yabawa rundunar ƴan sanda bisa ware dakarun da zasu samar da isasshen tsaro yayin wannan zaben cike gurbi da ke tafe.