Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Bala Mohammed a matsayin gwamnan jihar Bauchi.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da APC da dan takararta Sadique Abubakar suka shigar na kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da na kotun sauraron kararrakin zaben jihar Bauchi.
Kotun ta tabbatar da sakamakon kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben dan takarar jam’iyyar PDP, tare da yin watsi da karar da Abubakar ya yi na rashin cancantar ta.

Jim kadan bayan sanar da sakamakon kotun, Gwamna Bala Mohammed ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya yi wa Allah godiya kan wannan nasarar daya samu.

A watan Maris na 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Bauchi.
Daga nan Abubakar ya garzaya kotun domin kalubalantar sakamakon zaben.
A watan Satumban 2023, kotun ta yi watsi da karar da Abubakar da APC suka shigar.
Har ila yau awatan Nuwamba 2023, kotun daukaka kara ta tabbatar da Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.