A yayin da wa’adin da aka sa wa masu asusun banki na su tabbatar da sun mallaki lambar BVN da lambar NIN na katin dan kasa ke kara karatowa, akwai yiwuwar za a rufe asusun miliyoyin al’umma a fadin tarayyar kasar nan.

Idan za a iya tunawa, a ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 2023 ne Babban Bankin Najeriya ya bayar da sanarwa wa’adi inda ya umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoiyin huldar kudi su tabbatar da duk mai hulda da su mallaki lambar BVN da lambar katin dan kasa na NIN kafin ranar 31 ga watan Janairu na shekarar 2024.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, daga ranar 1 ga watan Maris duk wani mai asusun ajiyar da bai mallaki lambar BVN da NIN ba za a dora wa asusun alamar ‘Post No Debit or Credit’ ma’ana ba zai iya mu’amala da asusun ba gaba daya.

Wani bincike da wata cibiya mai zaman kanta ta yi ya nuna cewa, kashi 52 (miliyan 28) na mutanen da basu da asusun banki suna da lambar NIN yayin da kashi 5 na masu asusun banki basu da lambar BVN ko NIN.

Binciken ya kuma nuna cewa, ya zuwa shekarar 2021 akwai masu asusun banki miliyan 191.4 a Najeriya a ciki kuma miliyan 133.5 ke cikakken hulda dasu.

Haka kuma an samu masu BVN Miliyan 59.96 da suke da sususun banki a daidai ranar 18 ga watan Disamba 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: