Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a jam’iyyar APC ya ce ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan shari’ar gwamnan jihar a matsayin hukuncin Allah.

Gawuna ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar BBC Hausa.

Gawuna da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP sun yi ta shari’a bayan zaɓen gwamna a watan Maris na 2023.

A ranar Juma’a ne kotun ƙoli ta tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano.

A hirar da BBC ta yi da shi, Gawuna ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke hukuncin Allah ne, yana mai cewa ya amince da shi da gaskiya.

Ya kara da cewa ko a baya da INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe sun tayashi murna, haka zalika yanzu ma suna taya gwamna bisa samun nasara da ya yi a kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: