Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane Bakwai bayan da wani hatsari ya faru a jihar Osun.

 

Kwamandan hukumar Mista Henry Benamaisia ya ce hatsarin ya rutsa da wata motar haya da babur mai ƙafa uku.

 

Lamarin ya faru a safiyar yau wanda ya haɗa da maza huɗu yara huɗu.

 

Ya ƙara da cewa mutane huɗun sun mutu ne nan take.

 

Daga bisani kuwa kuma mutane uku su ka mutu bayan da aka kaisu asibitin koyarwa na jihar.

 

Kwamandan ya shawarci matuƙa ababen hawa musamman masu babur mai ƙafa uku da su kansance masu bin doka da oda don tseratar da rayuwar mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: