Rahotanni daga jihar Neja sun nuna cewar mutane da dama aka rasa bayan da wani jirgin ruwa ya yi hatsari.

 

Al’amarin ya faru a ranar Litinin kuma jirgin ke ɗauke da mutane sama da 100.

 

Jirgin ya taso daga Duggan Mashaya da ke ƙaramar hukumar Borgu, kuma ya nufi kasuwar Wara a jihar Kebbi.

 

Babban darakta a hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Abdullahi Arah ya ce jami’an su na ci gaba da ƙoƙari domin ceto mutanen da aka rasa.

 

Ya ce sun samu rahoton a ranar Litinin da ƙarfe biyu na rana, kuma su na ƙoƙari don ganin an ganosu.

 

Ya ce har yanzu babu rahoton rasa rai an hukumance, sai dai su na ƙoƙari don gano mutanen.

 

Ko a watan Nuwamban shekarar 2023 sai da wani jirgi ya yi hatsari da mutane 34 ciki har da wasu ƙananan yara goma a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: