Kotun ƙoli a Najeriya ta jingine hukuncin zaben gwamnan jihar Taraba tare da shirin yanke hukunci a gaba.

Kotun mai alkalai biyar, bisa jagorancin mai shari’a Justice Kudirat Kekere-Ekun ne su ka bayyana haka a yau Laraba.


Ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar NNPP Yahaya Sani ne ya ƙaulubalanci nasarar gwamnan.
Gwamna Kafas Agbu na jam’iyyar PDP aka ayyana a matsayin wand aya lashe zaɓen gwamna a jihar.
Ko a baya, sai a kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar gwamna Kefas Agbu na jam’iyyar PDP.
Zuwa nan gaba, kotun za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci a kan zaɓen gwamnan Taraba.