Hukumar kula da aikin ɗan sanda a Najeriya ta ce zuwa yanzu mutane 136,177 ne su ka nuna sha’awar shiga aikin tun bayan sanar da ɗaukar sabbin ma’aikata.

An fara tantancewa ne a ranar 8, ga watan Janairun da mu ke ciki.


Mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce an ɗora bayanan masu neman aikin su 108,768 yayin da ake aikin dora bayan sauran mutanen.
Mutane 416,270 ne su ka aike da bayanansu don samun gurbin shiga aikin.
Ya zuwa yanzu dai hukumar ta yi aikin tantance masu neman aikin a zahiri tare da gwaji na farko.
Matasa da dama daga jihohin Najeriya ne su ka halarci helkwatar ƴan sanda don tantancewa.