Wata babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ta dakatar da hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC daga cin tarar kafofin watsa labarai.

 

Justice Rita Ofili-Ajumogobia ce ta soke damar da hukumar ke da ita a baya, na cin tarar kafofin watsa labarai.

 

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar NBC ta ci tarar wani talabiji, bayan wasu bayanai da ya tattara dangane da ayyukan ƴan bindiga.

 

Wani lauya a Abuja Uche Amulu ne ya gabatar da ƙudirin a gaban kotun bayan samun sahalewa daga hukumar kare hakkin kafafen watsa labarai.

 

An gabatar da korafin ne ƙarƙashin dokar da ta baiwa kowa damar fadar albarkacin bakinsa.

 

Sai dai hukumar NBC ta ci tarar gidan talabijin ne bisa yanayi na tsaro da ƙasar ke ciki kamar yadda su ka bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: