Fitacciyar malamar addinin Muslunci Dr. Zahra U Muhammad Umar ta yi ƙarin haske dangane da manufar soke lefe da wasu al’adu na biki a jihar Kano.

 

Malamar ta ce soke lefe da sauran al’adu abu ne mai kyau domin hakan ba shi daa asali aa musulunci.

 

Ta yi tsokacin ne aa wani shiri da aka gabatar kai tsaye a shafukan Matashiya TV na YouTube da Facebook a yammacin yau Alhamis.

 

Hakan na zuwa ne bayan da wani lauya a Kano ya binciko wata tsohuwar doka wadda ta haramta yin abubuwa guda 18 ciki har da gara, lefe da yinin biki.

 

Sai dai malamar ta ce ya kamata gwamnati ta duba domin samar da mafita ga ma’aurata musamman wajen nuna wajabcin yin sutura ga mace, da kuma yin biki da bai saɓawa addini ba domin sunna ce.

 

Sannan ta ja hankalin jama’a da su kasance masu saukaka al’amura yayin aure domin samun albarkar da ke cikinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: