Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya gana da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa tare da jagororin jam’iyyar na jihar Kano.

Zaman da aka yi yau a fadar shugaban da ke Abuja ya samu halartar shugabanni da jagororin jam’iyyar na Kano.


Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano Nasiru Gawuna na daga cikin mutanen da su ka halarci zaman.
Hakan na zuwa ne ƙasa daa mako guda bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf a masayin halastaccen gwamnan Kano.
Sai dai babu wani bayani da ya fita dangane da batun da aka tattauna a yayin ganawar.