Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya ta bayyana takaicinta na fiecewar kasashen Nijar Burkina Faso da Mali daga ECOWAS.

Ma’aikatar ta bayyana cewa ba ta ji dadin ficewar kasashen uku ba daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wadda ake Kira da ECOWAS a takaice.


Kasashen da suka shafe sama da shekaru 50 a ciki sun bayyana ficewar su daga ECOWAS.
Kamar yadda ta bayyana ta ce har yanzu akwai dama ga kasashen uku da su zo don tattaunawa.
Sai dai masana na ci gaba da bayyana irin halin da kasashen Nijar Burkina Faso da kuma Mali za su shiga bayan fitarsu daga ciki.
Ana bayyana cewa kasashen suna da iyaka da kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS wadda hakan barazana ce ga harkokin kasuwancin kasashen uku.
Kuma hakan zai sanya wata alaka Mara dadi ga yan kasuwar manya da kanana a cewar masana.