Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara ta bayyana cewa wata gobara da ta tashi a kasuwar Gusau ta jawo babbar asarar kayan miliyoyi kudi.

 

Lamarin ya faru a ranar Talata da daddare da musalin karfe Tara a kasuwar Gusau dake jihar Zamfara.

 

Babban kwamandan hukumar reshen jihar Zamfara Hamza Muhammad ne ya bayyana haka ga menema labarai.

 

Da yake jawabi ga gidan Talabijin na channels ya bayyana cewa gobarar ta lakume dakiya mai tarin yawa da kuma wasu shaguna.

 

Sannan an samu rasa ran wani mutum wanda mamallakin shago ne ya rasu bayan kokarin sai ya kashe gobara da karfin tuwo.

 

Hamza ya ci gaba da cewa mutumin da ya rasa ransa ya rasu ne bayan da ya shiga shagonsa da nuffin kashe wuta a yayin da yan kwana-kwana su ke ƙoƙarin kashe wutar.

 

Sai dai babban kwamandan bai bayyana menene ya jawo sandin faruwar gobara ba ya zuwa yanzu.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: