Shugaban kungiyar yan canjin kudi na kasuwar Wapa ta jihar ya bayyana irin kalubalen da suka dade suna fuskanta a kan faduwa da tashin Dalar Amurka.

Shugaban kasuwar wafa ta jihar kano Sani Dada ne ya bayyana haka ga gidan talabijin na matashiya Tv a safiyar yau.

Ya ce sama da shekaru uku gwamnatin kasar ba at bayar da dala ga yan kasar

Ya ci gaba da cewa sun dauki matakin tsagaita cin kasuwa zuwa awanni biyar a kullum ne domin daidaita farashin dalar a kasuwa.

Ko a yau sai da dalar ta sauka da naira 30 inda ake siyar da ita a kan naira 1,500 kamar yadda ya shaida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: