Tsohon babban akanta na kasa Najreriya Ahmad Idiris ya bayyana cewa hukumar EFCC ta ci amanarsa bayan ta nemi ya bayyana sunan wasu gwamanoni a badakalar kudi daga bisani ta wanke shi daga tuhuma.

Ahmad Idris ya bayyana haka ga manema labarai a ci gaba da sauraron shari’arsa a gaban kotu.


Akanta wanda ake tuhuma akan badalar makudan kudade sama da biliyan 109,3.
Sai dai a wata tattaunawa da ka ayi da akanta Idris ya bayyana cewa hukumar dake bincike da yaki da masu yi wa tattalin arzkin kasa ta’anati ta kasa EFCC ta yaudare shi bayan wani bayanai daya bata na sirri.
Ya ci gaba cewa EFCC ta nemi da ya ba ta bayanai akan wasu gwamnonin kasar da kuma wata minista wanda ke da alaka da wawure wasu kudade.
Sai dai ya ce sun yi masa alkawarin za su wake shi daga tuhumarsa kudaden
Da yake jawabi ga jaridar Vangaurd Ahmad ya ce ba a tabbatar masa da alkawarin da akai masa ba.
Ahmad Idirin shi ne tsohon akanta na kasa wanda ake zarginsa da wasu mutane hadi da wani kamfani sun wawure wasu kudade masu yawa.
Hukumar dakile masu yiwa tattalin arzkin kasa ta’anati EFFC ta fara bincike akansa tare da gurfanar da shi a gaban kotu a watan maris a shekarar 2022