Kwamitin dake kula da ganin watan hadi da harkokin nisabin zakkah da na sadakin a Najeriya ya bayyana cewa sadaki ya koma naira 99,241 a bana.

Cikin sanarwa da kwamitin na duba ganin wata ya yi ya ce 99, 241 ne sadaki.


Kwamitin wanda sarkin muslmi ke jagoranta ya bayyana haka a yau safiyar Asabar a shafinsa kamar yadda kullum ya saba.
Sai dai ana ganin tashin da sadakin ya yi na goron zabi yana da alaka da faduwar darajar Naira.
A kwanakin baya dai sadaki ya koma naira 70,000 a kasar.