Wata kungiyar a jihar Kano mai suna yan Dangawale ta rubuta wasika ga gwamnatin jihar don mayar Tsohon sarki sunusi Lamido.

Wasikar da kungiyar ta rubuta haka a jiya Talata ta bayyana cewa ta na neman gwamnati ta rushe masarautu biyar da aka kirkiro.
Cikin sakon da wasikar ta aikewa da gwamnatin kano sun bayyana cewa dokar ta na bukatar gyaran fuska.

Sannan rushe masarautu biyar din jihar Kano ne za samu cikakken zaman lafiya a Jihar.

Masarautun Jihar Sun hada da na ta birnin Kano Rano Gaya karaye da kuma Bichi.
A ranar biyar ga watan Disambar shekarar 2019 ne dai gwamnatin jihar karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kawo tsarin masarautu biyar.
Sai dai majalisar jihar nan take ra amince da dokar Kuma aka tabbatar.
Amma alummar jihar tun bayan da aka Abba Kabir Yusif ya samu nasara a kotun koli ake yada cewa sabon sarki sabon gwamna.