Majalisar dokoki a Ghana ta yi fatali da ƙudirin sassauta hukunci a kan masu yin luwadi.

Wani ƙudiri da aka gabatar a gabatanta na neman sassauta dokar ga masu aikata luwadi bai samu karɓuwa ba.

Mataimakin masu rinjaye a majalisar ne ya gabatar da ƙudirin da ya buƙaci a yi wa dokar gyaran fuska, kuma ya bukaci a yi hakan a asirce.

Duk da haka bai samu goyon bayan masu rinjaye a majalisar ba.

Ƙudirin ya janyo ce-ce-ku-ce a zauren majalisar bayan da aka gabatar da wani ƙudiri da zai haramta neman jinsi a ƙasar.

An tafka muhawara a kai wanda za a ci gaba da yi zuwa gobe Alhamis.

Leave a Reply

%d bloggers like this: