Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya kwastam ta fara gwanjon kayan abincin da ta kama don saukakawa jama’a.

Shugaban hukumar a jihar Legas Mista Adewale Adeniyi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Legas.


Ya ce daga cikin bayanan da ake buƙata kafin samun tagomashin akwai lambar ɗan ƙasa ta NIN sannan a aikewa da mutum lambar da zai ƙarbi abincin.
Hukumar ta karyar da ƙaramin buhun shinkafa kan kuɗi naira dubu goma.
Kwamandan hukumar ya ce za a buɗe wuraren rijistar a wurare don saukakawa mabukata.
Ya ce manufar yin hakan an yi ne don karyar da farashin kayan abinci da ya yi tashin gwauron zabi aa ƙasar.
Idan ba ku manta ba, a labaran da mu ka kawo muku mun shaida cewar hukumar ta ce za ta rabar da kayan abincin da ta kama don saukaka hauhawaar kayan abinci da ake fama a Najeriya.