Ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakabawa ƙasashen Nijar Mali da Burkina Faso

 

Ƙungiyar ta ce ta yi haka ne don buɗe kofa samar d adaidaito daa kuma gabatowar watan azumin Ramadan.

 

Kuma an dage takunkumin da aka kakabawa Guinea Bissau.

 

Sannan ta bukacesu da su zo don a zauna a teburin sulhu.

 

A wani zama da shugabannin ƙasashen da ke ƙarƙashin ECOWAS su ka yi a yau, zaman ya mayar da hankali ne kan ƙalubale da nahiyar ke fuskanta.

 

Shugaban ƙungiyar Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalar da nahiyar ke fuskanta abu mafi muhimmanci a garesu shi ne samun haɗin kai.

 

Ya ce haɗin kai da su ke fata shi ne zai samar da zaman lafiya mai dorewa da kuma bunƙasa arziƙi a ƙasashen.

 

Ƙungiyar ta mayar da hankali ne a kan batun ficewar da ƙasashen uku su ka yi wanda ya ɗauki hankalin duniya.

 

Ƙasashen Nijar Mali da Burkina Faso dai na ƙarƙashin mulkin soja, wanda su ka fice daga kungiyar bayan zaman da su ka yi tare da cimma matsaya.

 

Batun ficewar ƙasashen ya girgiza ƙungiyar, wanda ko a taron shugabannin ƙasashen Afrika da aka yi a Habasha, sai dai aka tattauna batun.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: