Jam’iyyar APC a Jihar Rivers ta bukaci da gwamnan Jihar Siminalayi Fubara da ya yi murabus daga kan mukaminsa na gwamnan Jihar bisa gaza aikata abinda ya dace ga al’ummar Jihar.

 

Shugaban Jam’iyyar Cif Tony Okacha ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wata ganawa da manema labarai a Jihar.

 

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya zargi gwamna Fubara da sabawa dokokin kundin tsarin mulkin Kasa, tare kuma da gabatar da gwamnatinsa ba tare da yin kasafi ba.

 

Kazalika Tony ya sake zargin Fubara da kin kafa kwamitin da zai yi aikin gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar.

 

Shugaban na APC na Jihar ya kuma sake zargin Fubara da rike kudaden kananan hukumomi 23 na Jihar wanda ake ba su kowanne wata.

 

Tony yace gwamnatin ba ta da ikon da za ta rikewa kananan hukumomi kudadensu, wanda hakan ya sabawa dokokin Kasa.

 

Shugaban ya jam’iyyar ya ce matukar Fubara ba zai iya jagorantar Jihar ba, ya sauka ya bai’wa wanda zai iya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: