Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a jihar Kogi.

Sannan rundunar ta hallaka mutane biyu a Zamfara da kuma kashe wasu biyu a jihar Taraba.


Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Onyema Nwachukwu ya fitar a yau Juma’a.
Ya ce jami’an nasu sun kashe ƴan bindiga biyu ne a ƙaramar hukumar Baki ta jihar Taraba yayin musayar wuta.
Sai kuma wasu ƴan bindiga da jami’an nasu su ka kashe a yankin Kuyambana a jihar Zamfara.
Ya ce sun lalata sansanin ƴan bindigan da ke ɓoye cikin daji.
Ya ƙara da cewa sun kuma samu nasarar kuɓutar da wasu mutane yayin da ake ƙoƙarin yin garkuwa da su a jihar Kogi.
Nwachukwu ya ce jami’an nasu na aiki tuƙuru don ganin an samar da zaman lafiya a Najeriya.
