Rundunar ƴan sanda a jihar Bauchi ta tabatar da mutuwar ƙarin mutane uku bayan da aka gano wasu huɗu a yayin turmutsutsun karɓar zakka a jihar.

Mutanen sun rasa ransu ne a wajen karɓar zakka da ake bayarwa a jiya Lahadi.

Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar Ahmed Wakili ya tabbatar da mutuwar mutanen, wanda ya ce sun gano ƙarin uku daga ciki ne bayan tabbatar da mutuwar mutane huɗu.

Zuwa yanzu dai mutane bakwai rundunar ta tabatar da mutuwarsu a wajen raba zakkar.

Sai dai wani ɗan jarida da ke bibiyar lamarin y ace mutanen das u ka mutu sun kai su 17, yayin da aka samu wasu da su ka samu rauni.

Ko a jihar Neja ma wasu ɗaliban jami’a sun rasa ransu a makon jiya a wajen raba tallafin abinci.

Idan ba a manta ba, a jihar Legas ma wasu mutane sun rasa rayuwarsu, a wajen siyar da kayan abncin da hukumar kwastam ta kama kuma ta karyar da farashinsa wanda aka fara siyarwa a jihar.

An fara fuskantar ƙarin matsin rayuwa a ƙasar, tun bayan cire tallafin man fetur wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a jawabinsa bayan shan rantsuwar kama aiki.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: