Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami haɗi da fyaɗe ga matar aure a jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar AT Abdullahi ne ya bayyana haka yau Alhamis.


Ya ce an kama mutane uku bayan da su ka shiga gidan wani Mudan Ibrahim mazaunin ƙauyen Chori a ƙaramar hukumar Ringim tare da yi masa fashi daga bisani su ka yi wa matarsa fyaɗe.
Ƴan sandan sun samu labarin ne a ranar 17/03/2024.
Bayan zurfafa bincike, jami’an sun kama wani Umar Ibrahim, Umar Nasara, da wani Abubakar Isah dukkaninsu mazauna ƙauyen Chori a jihar.
Tuni aka ci gaba da zurfafa bincike a kai, kuma da zarar an kammala za su gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda kwamishinan ya shaida.
A wani labarin kuma kwamishinan ya bayyana nasarar kama wasu ƴan fashi da makami, da kuma wasu da ake zargi da aikata sata a jihar.