Rundunar ƴan sanda a jihar Delta ta miƙa Clement Ikolo ga sojoji bayan sanar da nemansa ruwa a jallo.

Clement Ikolo basarake ne kuma na daga cikin mutane takwas da rundunar ta sanar da nemansu ruwa a jallo a jiya Alhamis.


Basaraken ya miƙa kansa ga jami’an ƴan sandan jihar Delta bayan sanar da nemansa bisa zargin kisan sojojin Najeriya 17 da aka yi jana’izar su a ranar Laraba.
Helkwatar tsaro ce ta sanar da neman mutanen tare da fitar da hotunan fuakokinsu bisa zarginau da hannu a ciki.
Tuni aka damƙa basaraken a hannun helkwatar tsaro ta ƙasa yau Juma’a.
Mutanen takwas da helkwatar tsaro ta futar da hotunansu waɗanda take nema, ciki akwai maza bakwai da mace guda.