Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jami’an sojin Najeriya za su iya kawo karshen ‘yan ta’adda a fadin Kasar matukar sun samu goyan baya daga ‘yan Kasar.

 

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, bayan kammala taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar NNPP a birnin tarayya Abuja.

 

Sanatan ya ce ‘yan kasar na da rawar da za su taka wajen kawo karshen matsalar a kasar matukar suka taimakawa hukumomin tsaro da bayanai a kan ‘yan ta’addan.

 

Kwankwaso ya Kara da cewa duk da gwamnatin tarayya ce ke da alhakin magance matsalar, suma ‘yan kasa Na da alhakin taimakawa wajen magance matsalar.

 

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa nasarar za ta samu ne ta hanyar hada kai da zaman lafiya a fadin Najeriy

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: