Babban bankin Najeriya CBN ya kori ma’aikatan sa guda 40 a wani ci gaba na sauya fasalin ayyukansa.



Mutane 40 da bankin ya kora a wannan lokaci mafi yawa na daga ɓangaren DFD.
Rahotanni sun ce daga ciki akwai wanɗanda su ke a ɓangaren kiwon lafiya.
Zuwa yanzu dai bankin ya kori ma’aikata 67 kenan.
Akwai daraktoci da mataimakansu a cikin waɗanda bankin ya kora daga bakin aiki.
A baya bankin ya kori ma’aikatan guda 27 wanda a yanzu ya sake korara 40 jimilla da su ka zama 67 kenan.
Takardar korar dai na da kwanan watan ranar Juma’a 4 ga watan Afrilu da mu ke ciki.