Jami’an soji na Operation Hadarin Daji sun kama wani kwamandan kungiyar ISWAP mai suna Saidu Hassan Yellow.



Saidu Hassan wanda aka fi sani da Abu Saidu ya jagiranci hare-hare da dama a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
An kama kwamandan ne a jihar Adamawa sannan aka kwato wayoyin hannu guda uku, katin cirar kudi guda uku, makullai da kuɗi naira 1900.
Abu Saidu na dagaa cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo.
Kuma an kamashi ne a babbar kasuwar Mubi a ranar 9 ga watan Afrilun da mu ke ciki.
Tuni aka garzaya da shi zuwa babban sashen binxike na rundunar sojin don fadada bincike a kansa.
Ko a waatan Nuwamba na shekarra 2021 ya jagoranci harin ya yi sanadiyyar rasa rayuwar wasu sojoji a garin Askira.