Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da umarnin gaggawa na fitar da naira biliyan 1.1 domin kara sayo kayan abincin da za a sayarwa da ma’aikatan Jihar.

 

 

 

Kwamishinan yaɗa labarai matasa da wasanni da al’adu na Jihar Sagir Musa ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis.

 

 

 

Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar ta bayar da umarnin ne a yayin taron majalisar zartarwa da ya gudana a Jihar tun a ranar Litinin.

 

 

 

Musa ya kara da cewa gwamnatin ta yi hakan ne domin saukakawa ma’aikatan Jihar.

 

 

 

Kwamishanan ya ce daga cikin abubuwan da za a saya sun hada da buhunhunan shinkafa 12,000, da kuma kwalin taliya 15,000.

 

 

 

Sagir ya ce dukkan kayan za a sayarwa da ma’aikatan a cikin farashi mai sauki.

 

 

 

Kwamishinan ya bayyana cewa bayan sayo kayan gwamnatin za ta samar da shagunan hadin gwiwa a dukkan kananan hukumomin 27 na Jihar, domin ma’aikatan su dinga sayan kayan a ciki ta hanyar bashi tare kuma da biya kadan kadan.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: