Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan janye tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

 

Ministan ya ce sama da Naira tiriliyan 1 da za a samu sakamakon janye tallafin wutar lantarki, za a yi amfani da su wajen inganta samar wutar lantarki da ayyukan more rayuwa a ƙasar nan.

 

Jaridar The Nation ta ce Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a jiya lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin ‘Hannu da Yawa’ na Rediyo Najeriya da ke Kaduna.

 

Ministan ya ce wasu ƴan tsiraru masu hannu da shuni da kamfanoni ne kawai ke kwashe garaɓasar tallafin wutar lantarkin.

 

A cewarsa kaso 40% na tallafin wutar lantarkin yana amfanar kaso 15% da ke samun wutar lantarki ta sa’o’i 20 a kowace rana.

 

Idris ya jaddada cewa har yanzu kaso 85% cikin 100% na al’ummar da suke ƙarƙashin sauran rukunonin wutar lantarkin na samun tallafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: