Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mutum mai suna Lukman Adejoju bisa zargin kashe mahaifiyarsa dattijuwa mai suna Aminat.

 

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu cewa Lukman, mazaunin kauyen Kajola ne da ke kusa da Apomu a jihar Osun.

 

Rahoton ya bayyana cewa mutumin ya kashe mahaifiyarsa, wadda aka ce tana da shekaru kusan 100 a duniya, sakamakon takaddamar da ta shiga tsakaninsu kan manja.

 

Wani ganau mai suna Rasaki ya bayyana a ranar Lahadi cewa Lukman da mamaciyar sun dauki wani lebura ne wanda ya taimaka musu wajen siyar da wasu jarakunan manja.

 

Yayin da leburan ya dawo masu da kudin, an ruwaito marigayiya Aminat ta dage cewa sai dai a ba ta kudin, lamarin da ya harzuka dan nata Lukman.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: