Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu nasara a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

 

Babbar kotun ta jingine dakatarwar da shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, suka yi wa tsohon gwamnan na Kano.

 

Alƙalin kotun, mai shari’a Abdullahi Liman ya umurci shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, kada su yi aiki da umurnin babbar kotun jihar na dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

 

Mai shari’a Abdullahi ya kuma ya hana duk waɗanda umurnin babbar kotun jihar ya shafa bin umurnin, har sai an saurari ƙarar da Ganduje ya shigar ta neman a yi masa adalci a saurari ɓangarensa.

 

Wannan umurnin dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan babbar kotun jihar ta amince da buƙatar shugabannin APC na mazaɓar Ganduje ta dakatar da tsohon gwamnan na Kano.

 

Shugabannin dai sun dakatar da Ganduje ne saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.

 

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan Afrilu domin sauraren buƙatar da Abdullahi Umar Ganduje wacce lauyansa Jazuli Mustapha ya gabatar a gabanta.

 

Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da Abubakar Daudu. Sauran sun haɗa da rundunar ƴan sandan Najeriya, kwamishinan ƴan sandan Kano, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), da hukumar kare farar hula (NSCDC)

Leave a Reply

%d bloggers like this: