Gwanatin jihar Borno ta sanar da fara biyan daliban jinya da ungozoma tallafin karatu ga kowanne dalibi har N30,000 duk wata a fadin jihar.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya tabbatar da lamarin jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin bikin kaddamar da tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin Borno a Maiduguri, babban birnin jihar.


A cewar jaridar Daily Trust, gwamnan ya tabbatar da cewa dalibai 997 da suka fito daga jihar ne zasu mori tallafin.
Ya kara da cewa tallafin an yi shi ne ga daliban lafiya domin karfafa musu guiwa da samar da wadatattun ma’aikatan lafiya a jihar.
Jawabin nasa ya nuna gwamantin za ta kashe jimillar N1.3b a kan daliban a matsayin tallafi.
Mai girma gwamnan ya kuma bayyana cewa tallafin ya shafi kudin makaranta da alawus da za a rinka basu duk wata.
A cewar gwamnatin, daliban zasu rinka karban alawus din ne daga shekarar da suka fara karatu har su kammala.
Gwamnan kuma ya yi alkawarin bada aiki nan take ga dukkan daliban da suka nuna bajinta a lokacin karatun nasu.