Hukumar kula da samar da wutar lantarki ta kasa NERC ta bayyana cewa babu wani tabbaci akan dawo da tallafin kudin wutar lantarki da aka cire a Kasar.

Shugaban hukumar Sanusi Garba ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a yayin wata tattaunawa da majalisar wakilai ta kasa kwamitin da ke kula da wutar lantarki.
Shugaban ya shaidawa kwamitin majalisar cewa kudin da gwamnatin tarayya ke sanyawa a fanni wutar lantaki ba zai iya samar da wadatacciyar wuta a kasar ba.

Garba ya ce matukar aka ci gaba da zuba wa gwamnati idanu a harkar wutar lantarki babu shakka za ta iya durkushewa a kasar baki daya.

Hukumar ta ce matukar gwamnatin tarayya za ta dawo da tallafin a halin yanzu to ya zama wajibi sai ta kashe sama da naira triliyan uku a shekarar 2024 da muke ciki kadai.
Shugaban ya kara da cewa har kawo yanzu gwamantin ba ta gama biyan kudin tallafin shekarar 2023 da ta gabata ba, inda ake bin ta bashin sama da naira biliyan 400 kuma har yanzu ba a san ranar da za ta biya ba.