Wani Lauyan mai kare hakkin hakkin dan adam a Jihar Kogi Deji Ajare ya yi kira ga kakakin majalisar dokokin Jihar Umar Yusuf da su fara shirin tsige gwamnan Jihar ta Kogi Usman Ododo.

Lauyan ya bayyana hakan ne ta cikin wata takarda da ya aikewa da shugaban majalisar ta hannun magatakardar majalisar a ranar Juma’a.
Lauya Deji ya yi kiran ne bisa wasu zarge-zargen rashin da’a da kuma yin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba a Jihar.

A cewar Lauyan yin amfani da ayarin motocin gwamnan wajen boye tsohon gwamnan Jihar Yahaya Bello hakan ya sabawa ka’ida wanda kuma hakan ya kai ga ba mai laifi kariya da kuma yin amfani da dukiyar Jihar ta hanyar da ba ta dace ba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren yada labaran kakakin majalisar Muhammad Yabagi ya bayyana cewa magatakardar majalisar da shugaban majalisar ba su samu takardar da Lauyan ya aike musu ba.
Sakataren ya bayyana cewa har kawo yanzu majalisar ba ta ga wasu gamsassun hujjojin da za su sanya a yi yunkurin tsige gwamnan daga kan kujerarsa ba, kuma babu wata shaida da ta nuna gwamnan ya hana jami’an tsaro kama tsohon gwamnan Jihar Yahaya Bello.
Sakataren ya kara da cewa majalisar ta ce babu wani dalili da zai sanya su fara shirye-shiryen tsige Usaman Ododo.