Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukayide ya musanta zargin cewa shi ne ya fara bincikar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

 

A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, shugaban hukumar ya ce shi ma gadar binciken ya yi daga tsohon shugaban hukumar.

 

Shugaban ya ce ba shi da dalilin yi wa Yahaya Bello bita da kulli.

 

Ola Olukayode ya kara da cewa ya na kishin ganin an samu ci gaba a Najeriya, wanda a cikin watanni shidan fara aikinsa, hukumar ta kwato Naira biliyan 120 daga hannun ‘yan damfara.

 

Ya musanta cewa su na aiki da son zuciya tun bayan da ya kama aiki a shekarar 2023, inda ya ce idan ba su bibiyi shari’ar Yahaya Bello ba, ba za su iya bincikar kowa ba.

 

Shugaban EFCC ya kuma ce sun samu nasara a kotu kan wasu mutane 1600 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, wadanda tuni aka daure su.

 

A baya kun ji tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da yanzu haka ke fuskantar zargin sama da fadi da kudin al’ummarsa ya bayyana cewa ya na son a gurfanar da shi gaban kotu.

 

Sai dai lauyansa, Adeola Adedipa SAN ya bayyana fargabar umarnin da kotu ta bayar na a cafke shi, inda ya roki kotun ta soke umarnin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: