Hukumomi a Najeriya sun bayyana dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana a fadin ƙasar

 

 

 

Hakan ya biyo bayan zamewa da wani jirgi mallakin kamfanin ya yi daga titinsa a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Legas.

 

 

 

Ma’aikatar sufurin jiragen sama a Najeriya ce ta sanar da haka ta bakin sakataren dindindin Dakta Emmanuel Meribole a yau Laraba.

 

 

 

Ya ce dakatarwar na nufin tabbata da tsare rayuwa da lafiyar al’ummar ƙasar.

 

 

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa dakatarwar ta samu ne daga ministan sufurin jiragen sama wanda ya bayar da umarni nan take.

 

 

 

Ma’aikatar ta ce za ta gudanar da bincike a kai, da ma tabbatar da lafiyar jiragen domin al’ummar ƙasar.

 

 

 

A jiya Talata wani jirgin kamfanin Dana ya zame daga titinsa wanda hakan ya sanya fasinjojinsa cikin firgici.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: